A yau kuma zan nuna mana yadda ake hada pakijis (egg bondas ) ko kuma egg pacora (duk abu daya ne).
Abubuwan hadawa
- Kwai (dafaffe)
- Tarugu
- Filawa
- Seasoning
- Baking powder
- Gishiri
- Mai
Yadda ake hadawa
- Farko za ki tankade filawar, ki dama ta da ruwa kar ta yi tsululu kuma kar tayi kauri. Ki sa albasa, da lawashi, da seasoning a ciki ki juya.
- Ki dora mai a wuta, idan ya dauki zafi sai ki yi dipping kwai a cikin batter da ki ka hada ko ina ya samu sai ki sa a cikin ruwan mai ki soya.
- Za ki iya cire tarugu da su albasa idan baki so a ciki. Aci lafiya.
Sannan za a iya duba: Yadda ake hada spicy balls da yadda ake hada sausage scotch egg sauransu.
Photo Credit: Chef Fauzia