Skip to content

Yadda ake hada sausage scotch egg

Yadda ake hada sausage scotch egg
3.7
(3)

Ku karanta yadda ake hada sausage scotch egg daki-daki. Wannan recipe da duk wata mace za ta so gwadawa. Kar ki bari ayi bandake uwargida.

Abubuwan hadawa

  1. Ground beef sausage
  2. Kwai (dafaffe)
  3. Mangyada
  4. Maggi da seasoning
  5. Tarugu
  6. Albasa
  7. Flour
  8. kwai
  9. Gishiri

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki saye wannan ground beef chicken sausage (ana samu a super markets ko mall) sai ki dafa kwai ki cire bayan.
  2. Wannan ground sausage din sai ki zuba shi a cikin bowl ki saka tarugu da garlic da maggi ki motsa shi sosai har ya hade.
  3. Sai ki dinga diban hadin kina flat dinshi akan hannun ki, ki saka Kwai daya ki mulmula shi ya zama kamar ball a hannun ki sai ki barbada flour a kai ki aje. Haka za ki ci gaba da yi har ki gama. 
  4. Sai ki kada kwai ki saka gishiri a ciki. Ki dora mai a wuta ya yi zafi sai ki dinga dipping balls din cikin kwai kina soyawa. Idan ya soyu ya yi golden brown sai a kwashe. Za ki bar shi ya sha iska sannan ki yanka shi gida biyu kaman yadda ya ke a jikin hoton. A ci lafiya.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×