Skip to content

Yadda ake jollof mai hadi

Share |
jollof rice mai hadi
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

A yau za mu koya yadda ake jollof rice mai hadi. Idan mai karatu na biye da mu a girkinmu da ya gabata mun koyar da yadda ake jollof rice mai kwai, za a iya dubawa kafin mu ci gaba. To ga kuma jollof mai hadi dalla dalla:

Abubuwan hadawa

  1. Tafasashshen shinkafa
  2. Tarugu (ki jajjaga)
  3. Dafaffafen kayan ciki (ki yanka kanana)
  4. Albasa (ki yanka)
  5. Dankalin turawa (ki fere ki yanka shi kananna)
  6. Maggi
  7. Kayan gamshi
  8. Karas (ki yanka shi dogo dogo)
  9. Kwai dafaffafe (ki yanka kanana)
  10. Alaiyaho da water leave (ki gyara ki yanka)
  11. Man gyada

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko tukunya ki sa akan wuta sai ki sa man gyada ki zuba yankakiyar albasa ki soya sama sama.
  2. Sai ki dauko tarugu ki sa ki juya ki soya sama sama, dauko dafaffafen kayan cikin nan ki sa ki juya, ki kawo kayan kamshi da gishiri kadan, maggi iya dandano da zai mi ki, ki sa ki juya sai ki zuba ruwan dumi a ciki (iya wanda zai karasa dafa miki shinkafa).
  3. Ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya tafasa sai ki raba ruwan gida biyu. Dauko shinkafan (perboiled rice) ki sa a cikin tukunya ki kawo dankali ki sa sai ki dauko ragowar ruwan hadinki ki juye akai ki kara albasa ki juya a hankali sai ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya dauko shanyewa.
  4. Dauko Karas, kwai, ki sa akai ki juya ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin kadan. Sai ki kawo alaiyaho da water leave ki zuba a ciki sai ki juya a hankali ki rufe nadan wani lokaci har sai sun turara sai ki sauke. A ci dadi lafiya.

Photo Credit; Kathryn Doherty

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×