Skip to content

Yadda ake sponge pancakes

Share |
Yadda ake sponge pancakes
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

A yau zamu koyar da yadda ake sponge pancakes. Amarya na iya duba girkinmu na baya inda mu ka koyar da yadda ake red velvet pancake kafin mu ci gaba. To ga yadda ake sponge pancakes nan dalla-dalla:

Abubuwan hadawa

 1. Filawa cokali 4 (4 tbspn)
 2. Kwai 2
 3. Flavour cokali 1 (tspn)
 4. Man gyada cokali 2 babba (tbspn)
 5. Sugar 2 (tbspn)
 6. Madara ta gari cokali 2 (tbspn)

Yadda ake hadawa

 1. Da farko dauko flour ki tankade ki sa madara ta gari a ciki ajiye a gefe.
 2. Dauko mixer ki ki sa kwai a ciki ki bugashi sosai sai ki sa sugar ki bugasu tare har sai ruwan kwanki ya yi fari ya yi kauri.
 3. Sai ki kawo man gyada ko narkakke butter ki sa a ciki, ki juya da cokali ko karamin muciya, sannan sai ki zuba flavour a ciki.
 4. Sannan sai ki dauko flour (wanda ki ka tankade ki ka sa madara) sai ki rika sawa kadan kadan ki na juyawa har sai kin gama da flour din sai ki ajiye a gefe.
 5. Daura non stick pan akan wuta (kar ki cika wuta) idan ya yi zafi sai ki na diban kullin ki na zubawa a ciki sai ki rufe shi nadan wani lokaci (za ki ga ya fara kwai kwai a sama) sai ki juya dayan gefe shima ki gasa. Haka za ki yi ta yi har sai kin gama da kullin. A ci dadi lafiya.

Uwargida na iya sake duba Yadda ake Japanese pancake (doyaraki) da kuma Yadda ake egg rolls cikin sauki da makamantansu.

Rate the recipe.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading