Skip to content

Yadda ake japanese pancake (Doyaraki)

Share |
Yadda ake japanese pancake
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

A Yau da yardan Allah, a fannin girke girkenmu za mu koyi yadda ake Japanese pancake (Doyaraki). Amma kafin nan, mai karatu na iya duba girkinmu na baya inda mu ka koyar da yadda ake egg rolls cikin sauki. To mai karatu ga yadda ake pancake din na mu dalla dalla:

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi 1¼
  2. Kwai 3
  3. Madarar gari ¼kofi
  4. Ruwa ½kofi
  5. Baking powder 1½ karamin cokali (tspn)
  6. Flavor karamin cokali 1
  7. Zuma cokali 1
  8. Suga ?kofi

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko filawanki ki dan tankade a cikin kwano mai dan zurfi, ki sa baking powder, da madarar gari, sai ki juya, sannan ki ajiye a gefe.
  2. Dauko wani kwano daban ki fasa kwanki a ciki sai ki zuba suga, da zuma a ciki sai ki juya shi sosai har sai suga ya dauko narkewa.
  3. Sai ki dauko hadin filawanki, ki dauko garin kwanki shima ki juye akan filawa sai ki sa ruwa da flavour ki juya har sai ya hade jikansa ya yi sumul. Sai ki ajiye sa na minti 15 a cikin fridge.
  4. Bayan minti 15 sai ki dauko ki juya ki daura non stick pan na ki akan wuta (wutan ya zama kin rage shi sosai) idan ya yi zafi sai ki shafa mai kadan a cikin kaskon (kadan za ki shafa).
  5. Anan sai ki diba cokali 2 na kullinki ki zuba a cikin kaskon ki rufe da murfi nadan wani lokaci har sai kinga ya fara koyi koyi( bubbles) a saman sai ki juya dayan gefe shima ki gasa idan ya yi sai ki sauke. Haka za ki yi har sai kin gama da kullinki.
  6. Daga karshe sai ki dauko Nutella ki shafa a jikin daya sai ki sake dauko cake na ki ki daura akai (wanda ki ka shafa masa Nutella) za ki iya yanka shi kanana kanana yanda ki ka gani a hotonnan. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading