Skip to content

Yadda ake spicy cucumber salad

Yadda ake spicy cucumber salad
4.2
(5)

Ku koyi yadda ake spicy cucumber salad cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi bakwai ne da steps hudu kacal.

Abubuwan hadawa

  1. Cucumber
  2. Tumatur
  3. Albasa
  4. Koren tattasai
  5. Sauce na tarugu da albasa
  6. Soyayyen plantain
  7. Dafaffafen kwai

Yadda ake hadawa

  1. Ki sami cucumber ki wanke ki yanka. Ajiye a gefe.
  2. Dauko koren tattasai ki gyara ki yanka tare da tumatur na ki da albasa, kwai shima ki yanka.
  3. Dauko kwano ki zuba cucumber ki a ciki sai ki kawo albasa, tumatur, koren tattasai, dafaffafen kwai, soyayyen agada ki sa.
  4. Daga karshe ki kawo sauce na tarugunki da albasa ki sa a ciki kadan sai ki juya su hade jikansu sai ki diba ki zuba a gefen abinci kamar shinkafa da miya, jollof da dai sauransu.

Karin bayani

Kina gamawa ki sa a fridge don cucumber salad ba ya jimawa (soba da nan danan za ki ga ya fara fidda ruwa a jikinsa). A ci dadi lafiya.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×