A yau kuma bari mu duba yadda za ki hada hot spices hibiscus drink.
Abubuwan hadawa
- Ginger
- Cucumber
- Sobo (hibiscus)
- Abarba
- Sugar
- Pineapple flavour
Yadda ake hadawa
- Farko za ki gyara ginger sai ki wanke ta ki hada da abarba da ki ka yanka da cucumber sai ki sa ka su a blender ki saka ruwa, ki yi blending sosai ki tace shi ki aje gefe.
- Ki zuba sobo a cikin tukunya ki sa ruwa kadan ki dafa shi, idan ya dahu ki ajiye ya sha iska sai ki tace wannan sobonnaki.
- Ki hade ruwan ginger da sobo da ki ka tace, ki sa sugar, da pineapple flavour ko duk dandanon da ki ke so.
- Za ki iya kara tiara (berries ko strawberry daya).
Duba: Yadda ake hada apple smoothie da yadda ake hada papaya mocktail da makamantansu.