Skip to content

Yadda ake gasasshen kifi mai dankali

Share |
Yadda ake gasasshen kifi mai dankali
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Ga yadda ake gasasshen kifi mai dankali, mu koya ‘yanuwa. Cikin matakai kalilan uwargida za ki hada wannan kayataccen kifi.

Abubuwan hadawa

  1. Kifi
  2. Albasa
  3. Man gyada
  4. Tarugu ko yajin gari
  5. Dankalin turawa
  6. Tafarnuwa (garlic)
  7. Citta (ginger)
  8. Spices (Kitchen Glory, Benny, Mr Chef, Armor)
  9. Lemun tsami 
  10. Foil Paper

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki wanke kifin kaman yadda aka yi a na pepper soup na kifi amma ba za ki yanka shi ba sai dai Ki fasa cikin da kai kuma ki wanke ki cire dattin.
  2. Ki yanka dankalin ki soya shi sama sama ki aje gefe.
  3. Ki yi marinating na kifin. Yadda za ki yi marinating din shine ki sa spices, da seasoning, da garlic, da yajin gari ko tarugu a bowl ki sa spoon na man gyada biyu ki hada sai ki shafe kifin da shi har can ciki.
  4. Ki dora Kifin a saman foil paper sai ki dora akan tray na gashi.
  5. Ki dauko dankalin na ki ki cura a cikin kifin ki sa wani saman foil pepper ki yanka albasa sliced ki zuba a sama ki kwashe sauran hadin marinating ki zuba a sama.
  6. Ki gasa a cikin oven ko kuma ki dora foil din a pan ki yi gashin pan. Bayan kamar minti 35 ko 40 sai a duba idan ya yi sai a cire. Shi ke nan kifin ki ya hadu.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×