Skip to content

Yadda ake native jollof rice

Share |
Yadda ake native jollof rice
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake native jollof rice. Wannan Jollof rice ce ‘yar Nigeria gangariya (‘yan Ghana ma ku gwada), ba za ku so ku bari a barku a baya ba.

Abubuwan hadawa

  1. Tafasashshe shinkafa (perboiled rice)
  2. Dafaffafen ganda (ki yanka kanana)
  3. Kifi banda (ki jika da ruwan zafi)
  4. Stock fish (ki jikasa da ruwan zafi)
  5. Cray fish (ki nika)
  6. Shredded chicken (tsokar kaza)
  7. Tomatoes da tarugu (ki markada a blender)
  8. Albasa (ki yanka)
  9. Manja
  10. Curry leaves (ganyen curry)
  11. Ugu leave (ganyen ugu)
  12. Daddawa (ki daka)
  13. Spices (kayan kamshi)
  14. Maggi (iya dandanon da zai miki)
  15. Gishiri kadan
  16. Tarugu da tattasai (ki yanka su daban)
  17. Ruwan zafi (iya wanda zai karasa dafa miki shinkafan ki)

Yadda ake hadawa

  1. Daura tukunyarki akan wuta ki sa manja sai ki kawo albasarki ki soya sama sama sai ki dauko kayan miyanki ki sa (wanda ki ka markada) ki rufe tukunyarki na dan wani lokacin ki barshi ruwan ya dan shanye.
  2. Sai ki kawo dafaffafen ganda, daddawa ki sa ki juya ki barshi nadan wani lokaci sai ki kawo stock fish, kifi banda, tsokar kaza, cray fish ki sa ki juya kayan kamshi ki sa gishiri kadan, da maggi iya dandano da zai miki, ki juya ki rufe nadan wani lokaci har sai ya shanye.
  3. Bude tukunya ki ki zuba ruwan zafi (dai dai yanda zai karasa dafa mi ki shinkafa ) ki zuba sannan ki kawo tafasashshe shinkafa ki ki zuba sai ki kara albasa a ciki ki juya ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya shanye.
  4. Dauko ganyen curry ki sa ki kawo ganyen ugu ki sa ki juya ki rufe tukunyan, ki barsu su turaru sai ki sauke ki zuba a plate. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

Average: 2 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

3 thoughts on “Yadda ake native jollof rice”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading