Ku koyi yadda ake kunun couscous mai dadi ga kuma kyau. Wannan kunun yana da saukin hadawa. Ba a bawa yaro mai kiwuya.
Abubuwan hadawa
- Madara ta gari
- Couscous
- Sugar
- Flavour
- Ruwa
- Peak milk (badole bane)
Yadda ake hadawa
- Dauko madarar garin ki, zuba ruwa(daidai yanda ki ke son ya yi maki gardi) ki dama sai ki tace. Ajiye agefe.
- Daura tukunya akan wuta ki kawo madara ki zuba ki rufe, idan ya tafaso sai ki kawo couscous na ki ki zuba dan daidai.
- Ki rika juyawa a hankali har sai ya yi kauri, sai ki sauke ki kawo flavour ki sa ki juya sai ki zuba sugar ki juya.
- Ki zuba a bowl ko kofi. Daidai lokacin da za ki sha sai ki kawo peak milk ki zuba a kai. A sha dadi lafiya.