Skip to content

Yadda ake homemade gas meat

Share |
Yadda ake homemade gas meat

Mu koyi yadda ake homemade gas meat cikin sauki. Da wadannan kayan hadi guda takwas, uwargida za ki hada gas meat na ki gangariya.

Abubuwan hadawa

 1. Nama (marar kitse) rabin kilo
 2. Albasa
 3. Tarugu
 4. Maggi 4 ( Ko iya dandano da zai miki)
 5. Kayan kamshi
 6. Man gyada kadan (idan baki son mai ba dole sai kin sa ba)
 7. Gishiri kadan
 8. Koren tattasai

Yadda ake hadawa

 1. Ki gyara namanki  ki yanka shi kanana ki wanke sosai, ki gyara tarugunki da albasa ki jajjaga, sai ki sake yanka albasa da dan dama a wani kwano ki ajiye a gefe.
 2. Ki daura tukunya akan gas ko murhu ki sa namanki da ki ka gyara a baya ki sake yanka masa wata albasa kamar guda biyu sai ki sa kayan kamshi ki sa ruwan ki rufe tukunya nadan wani lokaci har sai ruwan jikin naman ya ragu sosai.
 3. Sai ki dauko tarugu ki sa, ki dauko yankakken albasa ki sa sai ki juya ki rufe tukunya. A nan sai ki rage wuta ki bar shi nadan wani lokaci har sai kinga ruwan yayi kauri namanki kuma ya yi luguf.
 4. Sai ki sake yanka albasa da koren tattasai kadan a wani kwano (amfani sa shi don ya gyara miki naman ki yayi kyau a ido) daf idan kinzo za ki sauke namanki sai ki sa ki juya sannan ki sa a plate.
Add to Lists (0)
ClosePlease loginn

No account yet? Register

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page