A yau zan koya mana yadda ake hada roasted beef. Harwa yau mai karatu zai iya duba daruruwan makalunmu da muka gabatar akan girke-girke.
Abubuwan hadawa
- Nama tsoka zalla
- Tarugu
- Albasa
- Tafarnuwa
- Seasoning
- Man gyada (2 spoon)
Yadda ake hadawa
- Farko za ki yanka naman ki bude shi ya yi fyale fyale sosai.
- Ki daka tarugu da albasa da maggi ki hada da garlic ki sa oil ciki.
- Ki shafe naman ki da wannan hadin sai a gasa na mintina 20. idan an gama sai a yanka irin yankan da ake bukata. A ci lafiya.
Za a iya duba: yadda ake hada pepper soup na kasusuwa da sauransu.