Skip to content

Yadda ake hada milky nut pap

Yadda ake hada milky nut pap
4
(3)

Ku koyi yadda ake hada milky nut pap. Wannan recipe ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!

Abubuwan hadawa

  1. Farar shinkafa ta tuwo
  2. Gyada
  3. Madara
  4. Dabino
  5. Sugar

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki jika farar shinkafa sai ki gyara gyada ki cire mata duk bawon bayan. Ki hada ta da shinkafa da dabino a nika sosai.
  2. Sai ki zuba ruwa ki tace shi. Wannan taceccen ruwan (kullun) da ki ka samu su zaki dora akan wuta ki na juyawa a hankali, amma kar a cika wuta.
  3. Za ki ga yana kara fari yana kauri. Idan ya yi dai dai sai ki sauke a zuba madara da sugar ko a bari sai idan za a sha.

Wannan kunun yana da dadi sosai ga karin lafiya. A sha lafiya.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×