Mu koyi yadda ake Indian fried rice cikin sauki, abubuwan hadawa guda sha hudu, cikin matakai guda hudu kawai!
Abubuwan hadawa
- Shinkafa (in son samu ne a sa basmati rice)
- Tarugu (chopped)
- Yankakkun ja da koren tattasai
- Lawashi (za ki bukaci mai dan yawa)
- Maggi
- Seasoning
- Gishiri
- Carrot
- Green peas
- Green beans
- Fennel Seeds
- Coriander
- Qwau Lemun tsami
- Mai ko bota
Ina fata uwar gida ta hadda komai ,
Yadda ake hadawa
- Ki sa mai a cikin tukunya, sai ki sa yankeken albasa ki idan ya yi zafi ki sa tarugu da slices na ja da green din tattasai ki juya kaman mintina sai ki sa lawashin albasa ki sake juyawa na kusan mintina.
- Sai ki sa karas, da peas, da green bean. Ki rufe ki bar shi kaman tsawon mintina biyar dan ya sulala a hankali ki sa duka seasoning, da spices da chillies na ki a hankali ki na zuba per boil rice ko basmati a ciki har sai ya hade.
- Idan kina yin na mutane da yawa ne dole za ki raba shi a wannan stage sai ki juya ki hade. Ki yayyafa ruwa ki barta ta gama dahuwa akan wuta ba sosai ba za ki fasa kwai ki zuba a ciki ki na juyawa har sai kwan ya hade.
- Ki matse lemun tsamin ki a ciki ki sake juyawa. Ki ci da irin salad din da ki ke so. A ci lafiya.