A yau kuma zan koya mana yadda ake hada desiccated coconut and chocolate chips cake. Uwargida ki shirya wannan cake din ba irin sauran cakes din da kika saba gani ba ne.
Abubuwan hadawa
- Butter(1)
- Sugar (1cup)
- Egg (8)
- Baking powder
- Chocolate chips (1 cup)
- Dessicated coconut(1cup)
- Filawa 2 cups
- Coconut milk
- Coconut flavour
Yadda ake hadawa
- Farko za ki buga sugar da butter sosai har ya hade.
- Sai ki fasa kwai daya bayan daya ki na hadawa.
- Ki zuba desiccated coconut da flavour da milk duka.
- Ki saka flour da baking powder ki hade.
- A zuba a tray na gashi har sai ya yi. Idan ya yi sai a ci.
Za a iya duba: sweet pancakes da sauransu.
(Photo Credit): homemadeinterest.com