Skip to content

Yadda ake hada cabbage sauce

Share |
Yadda ake hada cabbage sauce
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Mu koyi yadda ake hada cabbage sauce mai dadi da sauki, abubuwan hadawa guda tara, matakai guda hudu kacal.

Abubuwan hadawa

  1. Cabbage
  2. Green pepper
  3. Peas
  4. Green beans
  5. Tarugu
  6. Tattasai
  7. Seasoning
  8. Gishiri
  9. Man gyada

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki yi grating tarugu da tattasai da albasa ki yanka lawashi ki ajiye gefe.
  2. Ki yanka cabbage da green pepper su ma ki ajiye su gefe.
  3. Ki zuba man gyada a tukunya, idan ya yi zafi, sai ki zuba albasa ki juya. Ki zuba grated tarugu da tattasai dinki ki na juyawa. Za ki dan rufe na mintina biyu sai ki wanke veggies ki zub, amma ba da cabbage da albasa ba sune karshe. Ki juya ki sa seasoning ki sake rufewa.
  4. Za ki bude idan ya dahu, sai ki zuba cabbage da albasa. Ba a so cabbage din ya dafe sosai dan haka minti biyu sai ki sauke. Shima wannan sauce ana ci da abubuwa da yawa tun daga farar shinkafa, da chappati, phateera, har ma su jollof rice.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×