Flaky meat pie: Akwai hanyoyi da dama da ake yin meat pie. Amma a gare ni wannan hanyar ita ce best, akwai saukin yi sannan akwai dadi.
Flaky meat pie wani nau’in kayan ciye-ciye ne mai daɗi da ake yi da flour dough mai laushi da zalLan nama da kayan lambu a ciki. Ana yin dough dinne ta yadda zai kasance mai laushi kuma ya zamanto flaky bayan an gasa ko an soya shi.
Hakan ke ba shi ɗanɗano da kama mai kyau na musamman. Cikon naman da ke ciki ana haɗa shi da kayan ƙamshi da kayan lambu kamar su karas, dankalin turawa, albasa, koren tattasai da kuma kayan kamshi domin ƙara masa armashi da dadin ɗanɗano.
Flaky meat pie na daga cikin abincin da yara da manya ke so, kuma ana iya cin sa a matsayin karin kumallo, a wajen taruka, bukukuwa, da kuma matsayin abin ciye-ciye ko kayan marmari a kowane lokaci.
Abubuwan bukata:
1- 4 cups flour
2- 250g butter
3- 1 egg
4- 1 tablespoon sugar
5- 1 teaspoon baking powder
6- 1/2 teaspoon salt
7- 1/2 cup chill milk or water
For the filling
1- 1/2 kg minced beef
2- 1 onion
3- 1 spoonful pepper mix
4- Seasoning and spices to taste
5- Curry powder
6- 2 Irish potatoes
7- 2 carrots
8- 1 green bell pepper
yadda ake yi:
Abi wadannan matakai masu sauki dan samun flaky meat pie mai dadi da kayatarwa.
1- Za ki fara da hada meatpie filling dinki. Ki yi chopping ko shredding na kayan lambun ki na karas, albasa da koren tattasai da vegetable cutter dinki mai kyau ki ajiye a gefe. Ki zuba minced meat dinki, seasoning and spices a cikin pan, ki motsa har sai naman ya fara canja kala. Sannan ki zuba pepper mix dinki da curry ki motsa.
Sannan ki zuba dankalin turawan ki, karas, da koren tattasai ki motsa sannan ki bari su sulala na kar minti goma haka.

2- Idan za ki hada dough dinki, ki zuba flour a cikin bowl, sugar, gishiri, baking powder, egg, da margarine(kiyi amfani da margarine mai sanyi). Ki motsa har sai ya zama kamar breadcrumbs. Sai ki zuba madara ki karasa motsawa

3- Ki hada soft dough. Sai ki rufe shi ko kiyi wrapping dinshi da cling film ki saka a fridge na tsawon minti talatin. Kar kiyi kneading dinshi da yawa idan ba haka ba zai sa dough dinki yayi karfi da yawa.

4- Bayan minti talatin sai ki ciro shi daga fridge, ki raba shi kamar gida 4 haka sai ki fara rolling din su out. kar yayi kauri dayawa kuma kada yayi flat dayawa, dan daidai . Sai ki dora a kan meatpie cutter, ki zuba filling dinki a tsakiya, sannan ki rufe a hankali ki ciro shi.

5- Ki hada egg whites da madara kiyi mixing . Ki yi lining oven tray dinki da baking paper, sai ki jera meatpie dinki a kan oven tray din sannan ki shafe shi da wannan hadin da kika yi na madara da kwai.

6- Daga nan ki dauka ki saka a pre heated oven ki gasa da wutar sama da kasa na tsawon 30 minutes zuwa 40 minutes haka, ko kuma idan ya zama golden brown.

7- Shikenan meat pie dinki ya hadu cikin sauki duk da akwai hanyoyi da dama na sarrafa meat pie a fadin dunya. Zaki iya cin sa da cucumber juice ko da duk lemun da kike son ki hada da shi.
Aci dadi lafiya!





