Skip to content

Yadda ake farfesun kifi

Share |
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

A girkinmu na yau za mu koyi yadda ake farfesun kifi. Ga yadda ake farfesun kifin daki-daki: 

Abubuwan hadawa

 1. Kifi danye
 2. Tarugu
 3. Tattasai 
 4. Albasa
 5. Kayan kamshi
 6. Maggi
 7. Man gyada kadan
 8. Ganyen Curry
 9. Karas (ki yanka)
 10. Lawashi (ki yanka)

Yadda ake hadawa

 1. Ki gyara ki wanke kifin sosai ki yanka shi gunduwa gunduwa ki gyara tarugu ki da tattasai ki jajjaga sai ki ajiye a gefe.
 2. Yanka albasa ki itama ki ajiye a gefe, sai ki daura tukunyanki akan wuta ki sa man gyadanki kadan sai ki kawo jajjagen kayan miya tare da albasa ki sa ki juya ki kawo kayan kamshi, da maggi iya dandano da zai mi ki, ki sa ki juya.
 3. Anan sai ki zuba ruwan dumi (iya dai dai yanda ki ke son romanki ya kasance) rufe tukunya ki na dan wani lokacin kadan har sai ruwan ya tafasa sai ki kawo kifinki (wanda ki ka gyara a baya) ki sa a ciki Ki juya ki kawo ganyen curry ki sa (ana samunsa wannan ganyen a gun masu saida agushi) ki juya sannan ki kara yankakiyar albasa a ciki ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin kadan.
 4. In kifinki ya nuna, daga karshe ki kawo latas da ganyen albasarki (lawashi) ki sa a ciki ki juya sai ki kashe wuta ki barshi nadan wani lokaci ya turara sai ki zuba a kwano ko kula .A ci dadi lafiya.

Photo Credit; by Ifedayo Oni

Rate the recipe.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading