A girkin namu na yau zamu koyar da yadda ake coconut milk balls ne.
Abubuwan hadawa
- Kwakwa (irin na leda ko kanti)
- Madara ta gari
- Condensed milk
- Sugar
- Chocolate
- Mai kadan
Yadda ake hadawa
- Ki dauko kwanonki babba, ki zuba madararki a ciki ki kawo kwakwa ki zuba sai ki sa condensed milk a ciki ki kawo mai kadan ki sa.
- Sai ki kwaba shi ya kwabu sosai sai ki shafa mai a tafin hannu ki, ki na diba kadan kadan ki na fadada shi ki na sa chocolate a tsakiyan kina mulmula shi har sai ya baki ball. Haka za ki yi har sai kin gama da sauran kwabinki.
- daga karshe, sai ki barbada sugar a kai ki sa a fridge ya yi kamar minti 20, sai ki cire. Shi ke nan coconut milk balls na ki ya kammala. A ci dadi lafiya.
Wannan shine yadda ake coconut milk balls mai karatu. Na gode, sai Allah Ya hada mu a girki na gaba. Amma kafi nan, mai karatu na iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake cake mai kala uku da Yadda ake farfesun dankali da makamantansu.