Skip to content

Yadda ake farfesun dankali

Share |
Yadda ake farfesun dankali
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

A yau kuma tafe muke da yadda ake farfesun dankali, wannan romon dankalin cikin sauki za ki hada shi, biyo mu a hankali dan ganin namu salon.

Abubuwan hadawa

  1. Dankali
  2. Attarugu
  3. Tattasai
  4. Albasa
  5. Maggi
  6. Curry
  7. Mai
  8. Gishiri

Yadda ake hadawa

  1. Za ki tafasa dankalin da dan gishiri.
  2. Za ki markada kayan miyarki kisa a tukunya, sai kisa mai kadan ki soya kamar minti biyar.
  3. Sai ki sa ruwa rabin kofi da maggi, da gishi, da kuma curry
  4. Sai ki zuba dankalinki, ki tafasa kawai sai ki barshi kamar minti sha biyar.
  5. Sai a sauke a ci da maigida da yara.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×