Skip to content

Yadda ake cake mai kala uku

Share |
Yadda ake cake mai kala uku
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

A girkin namu na yau zamu koyar da yadda ake cake mai kala uku ne, da fatan mai karatu zai amfana da wannan sabon darasin.

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi 2
  2. Kwai 7-8 ( ya danganta da irin girmansu)
  3. Butter 1 (simas leda 1)
  4. Baking powder karamin cokali biyu (2 tsp)
  5. Flavour karamin cokali biyu (2 stpn)
  6. Sugar kofi daya (ko ki zuba iya zakin da zai mi ki)
  7. Food colour (purple, green da pink)

Yadda ake hadawa

  1. Da farko ki tankade filawarki tare da baking powder, sai ki ajiye a gefe. Ki sami mixer machine na ki, ki sa butter ki a cikin wannan kwanon sa (ko ki sami wani kwano daban idan da hand mixer za ki yi) ki yi ta motsa shi nadan wani lokaci. Ki kawo sugar ki sa a ciki ki yi ta motsa shi har sai sugar ki ya narke a ciki (wato ba ki jin gudajin sugar a cikin butter).
  2. Sai ki dauko kwai ki fasa ki yi ta motsa shi (kwan ana so ana sa shine daya bayan daya kuma ana motsa shi bayan kowani sa kwai daya) har ki gama da kwan na ki.
  3. Ki dauko filawarki da ki ka tankade tare da baking powder (za ki iya raba filawar gida 4 ) ki na zubawa a hankali a cikin wannan hadin butter har ki gama da flour ki na motsa shi.
  4. Sai ki dauko kwano guda 3 ki raba kullinki gida uku. Sai ki dauko food colour ki diga a kowani kwano (ko wani kwano kala daban). Ki juya ko wani kwano ajiye a gefe, sai ki dauko abun gashin (nakan sa takardar gashi a cikin abun gashin kafin na zuba kwallin cake din).
  5. Ki zuba hadin ko wani kulli (pink, purple da green) ki a cikin kowani takardar gashi kamar cokali daya (ba a so a cika shi don kar ya zube a lokacin gashi, ki sa su rabi rabi ko yadanfi rabi da kadan don ya yi gashi mai kyau).
  6. Sai ki sa a cikin magasa (prehated oven) ki gasa, har sai ya gasu (ko idan kinsa tsinke ya fito ba tare da komai ajikinsa ba) Sai ki cire ki bari ya sha iska, sai ki masa kwalliya yanda ki ke bukatansa. A ci dadi lafiya.

Wannan shine yadda ake cake mai kala uku. Na gode sai mun hadu a girki na gaba da yardan Allah. Amma kafi nan, mai karatu na iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake jollof mai hadi da kuma yadda ake jollof rice mai kwai da makamantansu.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×