Stick meat ko in ce tsire wani nau’in abinci ne da ya shahara a ƙasar Hausa. Ana yin sa ne da naman sa ko na rago da aka yanka kanana ko sala-sala, a saka su a kan tsinke icce wato wooden skewers ko na karfe, sannan a shafa musu kayan yaji kafin a gasa su a kan wuta. Tsire yana da ɗanɗano mai daɗi kuma ana yawan cinsa ne tare da albasa, tumatir, da sauran kayan lambu. Ana iya cin sa da sauran abinci irin su shinkafa, dambu, masa, biredi da sauransu.
Tsire ya kasance wani muhimmin ɓangare na al’adun Hausawa, musamman a lokutan bukukuwa, tarurruka, da kasuwanni. Yana ba mutane damar more dandanon naman da aka sarrafa cikin salo na musamman.
Abubuwan bukata:
1- 1kg tsokar rago
2- 1 tablespoon mixed spices
3- 1 tablespoon maggi powder
4- pinch of salt
5- 4 tablespoons vegetable oil
6- 3 tablespoons dakakken yaji
7- 1 teaspoon parsley flakes
Yadda ake yi:
1- ki yanka nama da fadi, sai ki zuba seasoning cubes da spices da mai ki motsa sosai yadda za su shiga ciki su hade da naman sosai.

2- A karamin bowl, ki zuba mai da yaji da parsley flakes ki motsa su.

3- ki samu skewers dinki ki jera naman a jiki. Idan wooden skewers zaki yi amfani da, preferably ki jika su tsawon 30 minutes zuwa 1 hour don kiji dadin soka su cikin naman ki.

4- kiyi arranging a kan oven tray sannan ki shafe shi da wannan hadin da kika yi na yaji. Daga nan sai ki dauka ki saka a air fryer oven ki gasa shi da wutar sama da kasa na awa daya ko kuma sanda kika tabbatar ya gasu.

5- Daga nan sai ki ciro kiyi serving. Ni dai na yi serving nawa da shinkafa da wake garau-garau amma zaki iya serving dinshi da party jollof rice, masa, dambun shinkafa ko duk abunda kike so kiyi serving dashi.

6- kiyi serving or plating dinshi akan plates masu uyau dan ya kara mishi presentation mai kyau.

7- Shikenan stick meat ko tsire ko kuma beef kebabs kamar yanda wadansu suke kiran shi ya hadu ya hadu.
Aci dadi lafiya!





