Skip to content

Yadda ake party jollof rice

party jollof rice 1
0
(0)

Party jollof rice wato jollof rice na biki yana daga cikin shahararrun abincin da ake yi a lokutan bukukuwa da taruka musamman a ƙasashen Afirka ta Yamma. Wannan abinci yana da ɗanɗano mai daɗi da ƙamshi wanda yake sa mutane da yawa su so shi. Ana yin sa ne da shinkafa, tumatir, tattasai, albasa da kayan yaji da kayan kamshi iri-iri tare da nama ko kaza. Girkin jollof rice na biki yana buƙatar kulawa da amfani da ingantattun kayan haɗi domin samun dandano mai kyau da abinci mai armashi.

Akwai hanyoyi da dama na sarrafa jollof rice, duk da cewa da yawan mutane musamman maza, su kan ce ba su son ta, sai dai da yawansu rashin son ya samo asali ne da rashin iya sarrafa ta. A yau na kawo maku hanya mai sauki kuma mai dadi, wadda idan kuka bi ta, za ku ji dadi.

Abubuwan bukata:

1- 3 cups rice

2- 2 cups pepper mix (tattasai, tarugu, tumatur, albasa)

3- 1 sachet tomato paste

4- 6 cubes maggi and onga

5- 2 tablespoons margarine

6- 1 teaspoon ginger and garlic paste

7- 6 bay leaves

8- 1/2 cup oil

9- 1 teaspoon salt

10- 1 tablespoon jollof mix (Spicity and maggi)

11- 1 large carrot

12- 4 cups water (or as required)

13- 1 onion

Yadda ake yi:

1- ki zuba mai a cikin kyakkyawar non stick pot, sai ki saka ginger and garlic paste, ki saka albasa da bay leaves, ki saka tomato paste dinki na tasty tom, sannan ki soya sama sama da wuta kadan. Daga nan sai na kawo pepper mix wanda already na dafa su sannan na markada.

party jollof rice 2

2- Sai ki zuba gishiri, seasoning, da kuma jollof mix dinki masu kamshi sannan wanda suke ja sosai saboda kalarta ta fita da kyau.

3- Bayan kamar minti biyar suna soyuwa, sai ki zuba wankakkiyar shinkafarki, ki zuba ruwa da diced carrots. Daga nan sai ki rufe ki bari ta dahu.

party jollof rice 4

4- idan ta dahu sai ki bude ki saka margarine, ki rage wutar sosai. Bayan minti biyar sai ki bude. Ki yi serving da abin da kike so kamar grilled chicken.

party jollof rice 5

Za’a ya cin ta da apple lemon fizz, carrot juice ko duk abinda ake so a ci dashi. Shikenan party jollof rice dinki ya hadu.

Idan kuna neman first class kayan kitchen, ku duba Bakandamiya shopping. Cikin rangwame da rahusa.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×