Skip to content

Yadda ake spinach soup

Share |
Yadda ake spinach soup
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ga yadda ake spinach soup cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi sha uku ne da steps biyar.

Abubuwan hadawa

 1. Alaiyaho
 2. Dafaffafiyar ganda
 3. Dafaffafen kayan ciki
 4. Dafaffafen kwai (ki bare bawon)
 5. Dafaffafen kifi
 6. Ganyen curry
 7. Albasa
 8. Dafaffen markadadden kayan miya
 9. Tumatur na gwangwani
 10. Kayan kamshi
 11. Maggi
 12. Man gyada
 13. Lawashi

Yadda ake hadawa

 1. Ki dauko alaiyahonki ki gyara shi ba sai kin yanka ba, sai ki wanke da gishiri ki zuba mishi tafasashshe ruwan zafi ki rufe nadan wani lokaci. Sai ki tace a colender. Ajiye a gefe.
 2. Daura tukunyanki akan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama. Sai ki kawo tumatur na gwangwani ki sa ki juya ki soya sama sama.
 3. Sai ki kawo dafaffafen kayan miya ki zuba a ciki ki juya ki rufe tukunyanki na dan wani lokacin.
 4. Dauko ganda, kayan ciki, kifi, kayan kamshi, maggi (iya dandano da zai miki ki zuba a ciki ki juya ki rufe tukunya nadan wani lokaci sai ki kawo dafaffafen kwanki ki sa ki juya.
 5. Dauko alaiyahonki ki sa a ciki ki juya ki kawo ganyen curry da lawashi ki sa ki juya kidan barshi ya turaru kadan sai ki sauke.

Ana iya cin wannann miyar da ko wani irin tuwo, kamar tuwon shinkafa da couscous da dai sauransu. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading