Skip to content

Yadda ake dafa couscous ta yi wara-wara

Share |
Yadda ake dafa couscous ta yi wara-wara
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ga yadda ake couscous ta yi wara-wara, mu koya ‘yanuwa. Sannin yadda za a dafa couscous ta yi wara-wara na da muhimmanci, uwargida.

Abubuwan hadawa

 1. Couscous
 2. Man gyada ko butter
 3. Tomato
 4. Koren tattasai
 5. Kwakwamba (Cucumber)
 6. Albasa

Yadda ake hadawa

 1. Da farko ki daura tukunya akan wuta ki sa ruwa ki rufe na dan wani lokaci
 2. ki dauko couscous na ki ki zuba shi a cikin kwano sai ki dauko man gyada ko butter ki zuba a ciki sai ki juya har sai man gyadan ya game jikinsa duka.
 3. Idan ruwa ya tafasa sai ki juye couscous naki a ciki sannanki rage wuta (Karki cika ruwa sosai)
 4. Dauko tumatir, albasa, koren tattasai da cucumber ki wanke ki gyara ki yanka su kanana sai ki sake wankewa da gishiri ki tsane su (kar kibar ruwa a jiki).
 5. Idan couscous naki yayi sai ki juye a wani abu(kwano babba) sai ki diba su tumatur da kwakwamba da ki ka yanka ki sa a ciki sai ki juya ki sa a a faranti.

Ana ci da Ko wacce irin miya (kamar miyar taushe, miyar stew da sauransu).

A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading