Skip to content

Yadda ake royal chips

Share |
yadda ake royal chips
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Uwargida ki koyi yadda ake royal chips mai dadi da alfarma. Wannan recipe ne da uwargida za ki hada shi cikn kalilan lokaci.

Abubuwan hadawa

 1. Dankalin turawa (soyayye)
 2. Kabeji (a yanka, a wanke)
 3. Kayan ciki (dafaffe)
 4. Tarugu (jajjaga)
 5. Karas  (ki yanka)
 6. Albasa
 7. Lawashi
 8. Butter
 9. Maggi
 10. Kayan kamshi

Yadda ake hadawa

 1. Daura tukunya akan wuta ki sa butter ki yanka albasarki ki soya sama sama. Sai ki dauko tarugu ki sa ki soya sama sama, kayan kamshi, maggi ki sa iya dandano da zai mi ki, sai ki juya ki sa ruwa kadan ki rufe nadan wani lokaci.
 2. Dauko kayan ciki ki sa ki juya, rufe nadan wani lokaci.
 3. Dauko kabejin, karas, lawashi, ki sa ki juya, rufe nadan wani lokaci sai ki dauko soyayyen Dankalin turawa ki sa ki juya nadan wani lokaci har sai ya hade jikansa. Sai ki sauke ki zuba a plate. A ci dadi lafiya.

Ana iya cin royal chips don karin kummalo (breakfast) a hada da kunun waken soya ko kunun gyada ko shayi da dai duk abin da mutum ke bukata. Na gode, sai mun hadu a girki na gaba bi izinillahi. 

Rate the recipe.

Average: 2.6 / 5. Rating: 9

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading