Uwargida ki duba yadda za ki yi kunun gyada mai ban sha’awa ga dadi ga kyau. Wannan kunun gyada baya bukatan wasu steps masu yawa sam.
Abubuwan hadawa
- GyaÉ—a gwango biyu
- shinkafa
- lemun tsami ko tsami
- sugar
Yadda ake hadawa
- Aunty na da fari za ki wanke, ki gyara gyaɗar ki, ki jiƙa ta.
- Sai ki dauko shinkafar ki da ki ka gyara ki ka wanke, sai ki haÉ—a waje É—aya da gyaÉ—arki.
- Daga nan sai ki ba da a markaɗo miki, bayan an kawo sai ki tace, ki ɗaura tukunya a wuta ki zuba ƙullun ki ringa juyawa da muciya har sai yayi kauri yanda ki ke so.
Sai ki sauke idan kin sauke sai ki matsa lemun tsami ko tsaminki, za ki ga ya yi fari tas ya yi kar kar kamar nono, se ki zuba suga sai sha.
Allah ya biya