Skip to content

Yadda ake red velvet cake

red velvet cake 1
0
(0)

Yadda ake red velvet cake wani nau’in cake ne na musamman wanda aka fi sani da jan kalarsa mai kayatarwa. Wannan cake din ya shahara sosai a duniya saboda kyawun bayyanarsa da kuma ɗanɗanon da yake da shi. Ana yawan amfani da shi a bukukuwa kamar bikin aure, ranar haihuwa, da sauran tarukan farin ciki.

Red Velvet Cake ana haɗa shi na da sinadarai kamar fulawa, sukari, ƙwai, butter, madara, da cocoa powder tare da jan food color wanda yake bashi kyakkyawan jan kala. Wannan wani cake ne mai matukar dadi, wanda mutane da yawa suna yawan tambayar yadda ake yin shi. Yana da sauki sosai.

Abubuwan bukata:

1- 2 and 1/2 cups flour

2- 1 and 1/2 cups sugar

3- 2 eggs

4- 1 cup buttermilk

5- 1 cup vegetable oil

6- 1 teaspoon baking soda

7- 1 teaspoon white vinegar

8- 1 teaspoon red velvet powder

9- 1/2 teaspoon salt

10- 1 teaspoon strawberry flavor

11- 1 teaspoon milk flavor

Yadda ake yi:

1- ki fara mixing dry ingredients dinki

red velvet cake 2

2- Sai ki zuba mai da sugar a cikin bowl ki mixing. Sannan ki zuba kwai, flavor, da white vinegar ki mixing sosai har sai sun zama smooth.

red velvet cake 3

3- Daga nan sai ki kawo buttermilk dinki  ki zuba ki mixing da kyau

red velvet cake 4

4- Ki zuba flour da red velvet powder

red velvet cake 5

5- Ki mixing. Ga yadda batter din zai kasance.

red velvet cake 6

6- Ki zuba a cikin gwangwanin gashi wato baking pan da kike so.

red velvet cake 7

7- Then ki saka a cikin oven ki gasa da wutar kasa kawai a medium heat. Idan ya gasu, sai ki kunna wutar sama na minti biyar saboda saman ya yi kyau.

red velvet cake 8

Shikenan red velvet cake dinki ya hadu. Zaki iya cisa da hot spice hibiscus tea ko da duk irin lemu ko abun sha da ake so.

Aci dadi lafiya!

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×