Skip to content

Yadda ake plantain vegetable rice

Share |
yadda ake plantain vegetable rice
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake plantain vegetable rice ga dadi ga kuma kyau. Wannan plantain vegetable rice ba a bawa yaro mai kiwuya. Sai an gwada!

Abubuwan hadawa

 1. Tafashashshen shinkafa
 2. Agada (plantain)
 3. Karas
 4. Koren wake
 5. Tarugu kadan
 6. Tumatur
 7. Kayan kamshi
 8. Maggi
 9. Mai ko butterd
 10. Albasa
 11. Gishiri

Yadda ake hadawa

 1. Dauko plantain naki ki yanka kanana ki barbada gishiri kadan, sai ki daura mai a kan wuta ki soya shi ki tsane. Ajiye a gefe.
 2. Dauko tumatur, albasa ki gyara ki wanke ki yanka kanana ajiye a gefe.
 3. Daura tukunya akan wuta ki sa mai ko butter, albasa ki soya sama sama sai ki kawo tarugu kadan ki sa ki soya sama sama shima kawo kayan kamshi, da maggi, da gishiri kadan ki sa a ciki ki juya.
 4. Sai ki kawo ruwan zafi ki sa (iya dai dai wanda zai karasa dafa miki shinkafanki) sai ki rufe nadan wani Lokacin har sai ya tafaso sai ki kawo shinkafan ki sa ki juya sanna ki rufe nadan wani lokacin har sai ya shanye ruwan.
 5. Daga nan ki kawo karas, da koren wake (dama kin dan tafasa su tare da baking powder) ki sa ki juya ki barshi nadan wani lokaci daga karshe sai ki kawo soyayyar agada, da yankakkiyar albasa ki sa ki juya ki juya a hankali sai ki sauke ki zuba a plate. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading