Skip to content

Yadda ake kunun madara

Bookmark (0)

No account yet? Register

Ku koyi yadda kunun madara cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Wannan recipe na bukatan kayan hadi bakwai da kuma steps uku.

Abubuwan hadawa

  1. Couscous na kunu kofi daya da rabi
  2. Madarar gari kofi shida
  3. Ruwa babban kofin shan ruwa biyu da rabi
  4. Coconut milk kofi daya
  5. Ruwan kwakwa rabin kofi
  6. Flour (don daure kunun)
  7. Sugar yadda ake bukata

Yadda ake hadawa

  1. Ki samu tukunya ki dora akan wuta ki sa ruwa ba dayawa ba ki sa sugar idan ruwan ya yi zafi sai ki sa couscous, ki bashi kamar minti takwas ya nuna kada ki bari ya fara fashewa.
  2. Ki samu roba ki sa milk na ki ki dama da ruwa, ki sa coconut milk, coconut water ki juya su hade sai ki sa 2½ cup na ruwa ki sake mixing.
  3. Bayan 8 minutes din sai ki zuba mixture na ki a cikin tukunyar ki juya. Ki bari ya yi tashi kaman sau biyu. Ki samu karamin roba ki sa flour sai ruwa kadan ki dama ki tace, sai ki sa akan kunun don ya danyi kauri. Sai ki sauke bayan minti daya.

Karin bayani

Za ki iya shan kunun madara da zafinsa ko kuma za ki iya sa a fridge in ya yi sanyi ki sha.

Idan ki ka sake daura kunun madara akan wuta dan ya dumamu zai salamce.

How many stars is worth this recipe?

As you found this recipe interesting...

Follow us on social media to see more!

Share this recipe on social media.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free recipes remaining!
×