Mu koyi yadda ake hada savoury stuffed yam balls cikin sauki. Kayan hadi guda bakwai sannan matakan hadawa guda shida kacal.
Abubuwan hadawa
- Doya
- Tarugu
- Nama (ground beef)
- Seasoning
- Breadcrumbs/flour
- Kwai 2
- Albasa da lawashi
Yadda ake hadawa
- Da farko za ki fere doya ne sai ki dafa ta har ta dahu. Ki cire ta ki tsane ruwanta sannan sai ayi mashing dinta ko a dan daka ta a turmi.
- Ki saka tarugu, da lawashi da albasa a ciki.
- Ki cire yolk na kwai ki sa shi a ciki ki ajiye whites din a gefe.
- Ki saka salt da seasoning na ki sai ki hade shi sosai ko ina ya ji.
- Sai ki dinga sawa a tafin hannunki ki sa stuffing na naman ki ko kaza ko ma kifi. Ki rufe shi kaman ball.
- Sai Ki dora mai a wuta ki sa salt ki kada egg white dinki. Za ki sa balls din a cikin Breadcrumbs sai ki tsoma a cikin ruwan kwai ki sake sawa a breadcrumbs sai cikin mai a soya. Idan baki da breadcrumbs za ki iya amfani da filawa. A ci lafiya.