A yau zamu koyi yadda ake hada local jollof rice wato dafadukan shinkafa ke nan da Hausa.
Abubuwan hadawa
- Shinkafa
- Tattasai da tarugu
- Daddawa
- Albasa
- Seasoning
- Manja
- Tafarnuwa
- Busashshen kifi
- Danyen nama
Yadda ake hadawa
- Farko zaki dora tukunya ki zuba manja a ciki ki yanka albasa. Sai ki wanke nama ki zuba a ciki.
- A dai dai wannan lokacin uwargida ta gyara kayan miya (tattasai tarugu da albasa) sai ki zuba a cikin wannan naman ki juya, za ki ga yana dan soyuwa sama sama, sai ki tsayar da ruwan dahuwar shinkafarki.
- Ki zuba tafarnuwa, daddawa da maggi da sauran seasoning a cikin ruwan sannan ki rufe.
- Idan ya tafasa sai ki wanke shinkafa ki zuba ki rufe. Ki yanka albasa manyan slices sai ki gyara kifi busashe ki hade su.
- Idan shinkafarki ta fara tsotse ruwa sai ki zuba ki rufe su dahu tare. Idan ya dahu a sauke.
Za a iya duba: Yadda ake hada onion sauce da yadda ake hada tuna muffins da sauransu.
Photo Credit: Immaculate