Skip to content

Yadda ake plantain sauce

yadda ake plantain sauce
4
(4)

Ku koyi yadda ake plantain sauce mai dadi ga kuma kyau. Wannan sauce na musamman yana da saukin hadawa. Ba a bawa yaro mai kiwuya.

Abubuwan hadawa

  1. Agada (plantain)
  2. Dafaffen kifi (ki bare ki cire kaya)
  3. Albasa (ki yanka)
  4. Mai
  5. Tarugu (ki jajjaga)
  6. Kayan kamshi
  7. Maggi
  8. Lawashi (ki yanka)

Yadda ake Hadawa

  1. Ki dauko plantain na ki ki bare ki yanka shi kanana (irin yankan da ki ke so) sai ki barbada gishiri kadan. Ajiye a gefe.
  2. Sai ki daura mai kan wuta ki kawo plantain na ki, sai ki soya har sai ya soyu ki kwashe ki tsane a matsani. Ajiye a gefe.
  3. Rage man da ki ka yi suya dashi a wani kwano sai ki kara mai da kaskon kan wuta (ki bar iya mai da zai mi ki sauce na ki a ciki).
  4. Sai ki sa tarugu, da albasa, ki juya sannan ki kawo kayan kamshi ki sa, da maggi iya dandanon da zai miki ki sa sai ki juya.
  5. Kawo kifin ki ki sa ki juya, sai ki kara albasa a ciki ki juya.
  6. Sai ki rufe na dan wani lokaci (ki rage wuta sosai).
  7. Daga karshe, ki kawo soyayyar plantain na ki ki sa tare da lawashi ki sa ki juya ki rufe nadan wani lokaci.
  8. Sai ki kwashe a zuba a plate. Ana iya cin wannan sauce tare da alale (moimoi), ko shinkafa, ko taliya da dai sauransu. A ci dadi lafiya

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×