Skip to content

Yadda ake hada KFC chicken

Yadda ake hada KFC chicken
3.1
(16)

Ku koyi yadda ake hada KFC chicken a gida. Makatai hudu kacal uwargida za ta bi ta kammala wannan kayataccen suyan kaza.

Abubuwan hadawa

  1. Kaza
  2. Flour
  3. Man gyada
  4. Bread crumbs ko cornflakes
  5. Kwai
  6. Maggi
  7. Albasa

Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki fara wanke naman kazar sai ki zuba shi a cikin tukunya.
  2. Ki saka spices dan cire karnin kazan ki yanka albasa a ciki ki rufe. Ya kamata Uwargida ta san cewa ita kazar turawa ba a saka mata ruwa ko a wurin tafashen ta.
  3. Idan ya tafasa sai ki cire ki tsane naman a cikin colander.
  4. Ki fasa kwai a cikin bowl ki aje gefe. Sai ki dinga saka wannan naman cikin flour sai ki saka a cikin ruwan kwai, sai ki saka cikin breadcrumbs ko cornflakes (wanda ki ka nika) sai a soya a cikin mai. Idan ya yi sai a sauke.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×