Egg into egg…
Abubuwan hadawa
- Kwai 5
- Albasa 1
- attarugu 1
- Tumatur1
- Dandano
- Gishiri
- Curry
- Busashshen biredi
- Mai
- flour
- Barkono
- Paprika
- Garlic powder(idan ana so)
Yadda ake hadawa
Abi wadannan matakai masu sauki dan hada egg into egg mai dadin gaske.
- A dafa kwai 4, a bari ya dahu gaba daya.
- Bayan sun dahu a bari su huce har sai sunyi sanyi.
- A bare kwan a yanke saman a hankali
- A yanka tumatir, attarugu da albasa a soya sama sama, a zuba dandano da gishiri yanda akeso.
- A cire kwanduwan kwayayen ,a hada a cakuda da albasa da attarugun da aka soya.
- A dunkula hadin albasar da kwanduwan a zuba a cikin farin kwan, a maida murfin a rufe.
- A tsoma dafaffen kwan a cikin garin flour da aka hada da paprika da garlic powder.
- Bayan nan sai a tsoma acikin kwan da aka kada, sannan a tsoma ko ayi rolling din shi acikin busashshen biredi(ana yi ana dan daddana shi dan ya kama ajikin kwan yanda ya kamata). Ayi ta maimaitawa har sai an rufe duka kwayayen gaba daya da busashshen biredin.
- A zuba mai acikin tukunyan suya mai dan zurfi yadda zai rufe abunda ake soyawa. A bari man yayi zafi dadai gwargwado, sannan sa a tsoma kwayayen a ciki ahankali.
- A bari su soyu amma ana yi ana dan jujjuya su dan kada suyi golden brown din iya gefe daya kawai.
- Bayan su soyu sai a kwashe ko a tsame su a zuba akan paper towels ko a kwando mai raga-raga a bari ya huce. a zuba ketchup ko hot sauce ko duk sauce din da ake so a kai ko a gefe aci dashi kamar dai yanda ake cin scotched eggs..
- Ana ya cin su da kunun madara, virgin chapman, apple juice ko makamantan su.
Aci dadi lafiya!






