Skip to content

Yadda ake gashin kifi karfasa

Share |
gashin kifi karfasa
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Na san da yawan mata na son koyon yadda ake saffara kifi ta hanyoyi daban daban. A dalilin haka yau mun kawo muku yadda ake gashin kifi karfasa (tilapia). Ku biyo mu domin ganin yadda ake wannan kayan armashin.

Abubuwan hadawa

 1. Kifi danye
 2. Maggi
 3. Masoro
 4. Citta
 5. Kanumfari
 6. Tafarnuwa
 7. Albasa
 8. Koren tattasai
 9. Attarugu
 10. Mai
 11. Foil paper

Yadda ake hadawa

 1. Za ki daka dukkanin kayan kamshin da muka lissafa a sama tare da attargu asa maggi da mai a cakude su gaba daya. Sai a shafe jikin kifin da shi (bayan an wanke kifi an tsane shi ke nan)

 2. Sai a sa a foil paper a sa albasa da koriyar tattasai sannan sai nade a saka a oven a gasa kaman na kimanin mintuna ashirin.
 3. Kafin a cire abude foil din sannan a sake mai da shi cikin oven din a bude ya sake gasuwa na wasu mintuna kaman goma haka. Shike nan kifinki ya yi, a kwashe a hankali. A ci dadi lafiya!  

Wannan gashi na da kyau da dadi, sannan kuma kamar yadda kuka sani kifi abinci ne da ke da amfanin gaske ga dan adam. Ko ba komai ai za ku gwada, ga dadi ga amfani ga jiki!

Za ku iya duba girke-girken na baya, kamar: toast bread da veggies da sauransu.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading