Skip to content

Yadda ake toast bread da veggies

Share |
toast bread da veggies
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Uwargida ki koyi yadda ake toast bread da veggies. Wannan toast bread da veggies yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Biredi mai yanka
  2. Nama(dafaffe)
  3. Butter ko mai
  4. Kayan kamshi
  5. Tarugu (ki jajjaga)
  6. Albasa (ki yanka)
  7. Kabeji (ki yanka) 
  8. Karas (ki yanka)
  9. Koren wake (ki yanka)

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko naman ki ki sa a turmi ki daka ki kwashe ki ajiye a gefe.
  2. Dauko kasko ki sa butter ko man gyada kadan sai ki yanka albasa ki soya sama sama, sannan ki kawo tarugu ki sa ki juya.
  3. Sai ki dan zuba ruwa kadan sannan ki kawo nama (wanda ki ka daka) ki sa ki juya.
  4. Sannan ki sa maggi da gishiri (iya dandanon da zai miki) kayan kamshi ki sa, sai ki juya ki rufe nadan wani lokaci.
  5. Daga karshe ki kawo su kabeji, da karas, da koren wake ki zuba ki rufe su dan turaru sai ki sauke ki ajiye a gefe.
  6. Dauko biredinki mai yanka ki shafa masa butter a gefe daya (haka za ki yi shafe jikin sauran biredin gefe daya daya) ajiye a gefe.
  7. Sai ki dauko abun gashi (toaster machine) sai ki dauko biredi (wanda ki ka shafa masa butter ta gefe daya) ki fara daura gefen da kika shafawa butter ta kasa.
  8. Sannan ki hadin nama ki ki zuba cikin biredin (ki daidaita shi tagun ramin guda biyu su zaki sawa hadin nama banda tsakiya).
  9. Sai ki dauko wani biredin ki rufe shi ta inda ba butter sai ki gasa haka za ki yi tayi har sai kin gama. A ci dadi lafiya

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×