Skip to content

Yadda ake fish egg sauce

Share |
Yadda ake fish egg sauce
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Uwargida ga yadda ake fish egg sauce cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Ana bukatan kayan hadi sha biyu da kuma steps biyar.

Abubuwa hadawa

 1. Kifi dafaffe (ki bare sala sala ki cire kaya)
 2. Kwai dafaffafe (ki yanka)
 3. Tarugu (ki yanka)
 4. Butter
 5. Man gyada kadan
 6. Tumatir (ki yanka)
 7. Koren tattasai (ki yanka)
 8. Ruwan silalenki kifi.
 9. Albasa
 10. Maggi
 11. Kayan kamshi
 12. Gishiri kadan

Yadda ake hadawa

 1. Daura tukunya ki akan wuta ki sa butter ki kawo man gyada kadan ki sa sai ki yanka albasa a ciki ki soya sama sama.
 2. Sai ki kawo tarugu ki sa ki soya sama sama sannan ki kawo ruwan silalenki kifi ki ki sa a ciki ki juya.
 3. Dauko kayan kamshi, maggi iya dandano da zai miki ki zuba a ciki ki juya da gishiri kadan ki sa ki juya.
 4. Sai ki dauko tumatir ki sa ki juya ki rufe nadan wani lokaci.
 5. Daga nan sai ki kawo dafaffafen kifin ki ki sa ki juya a hankali sai ki kawo dafaffafen kwanki ki sa ki juya ki rufe tukunya ki na dan wani lokacin kadan. Daga nan sai ki sauke. 

Ana iya cin wannan sauce da alala, taliya, shinka ko macaroni da dai sauransu. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading