Skip to content

Matakai 5 na yin Chinese macaroni

Share |
matakai 5 na yin chinese macaroni
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Mu koyi yadda ake Chinese macaroni cikin sauki kuma ba tare da bata lokaci ba. Uwargida kina bukatan kayan hadi guda tara ne kacal wajen hada wannan girki.

Abubuwan hadawa

 1. Tafasashshiyar macaroni
 2. Tarugu
 3. Tattasai (ki jajjaga)
 4. Albasa
 5. Kwai
 6. Butter
 7. Alaiyaho ko ganyen ugu
 8. Kayan kamshi
 9. Maggi

Yadda ake hadawa

 1. Ki sami kwano ki fasa kwanki a ciki sai ki yanka albasa a ciki da gishiri kadan sai ki bugashi, ajiye a gefe.
 2. Ki daura tukunya akan wuta ki sa butter ki a ciki ki barshi ya narke sai ki yanka albasa a ciki ki soya sama sama.
 3. Sai ki kawo kwanki ki sa a ciki ki soya (Za ki yi scrambling na shi ne kamar yanda ake na miyan kwai).
 4. Sai ki zuba tarugun da tattasai a ciki (wanda ki ka jajjaga) ki juya ki sai ki tsaida ruwa (ruwan dai dai wanda zai karasa dafa miki macaroni za ki sa kuma na dumi) sannan ki kawo kayan kamshi, maggi iya dandano da zai miki ki juya.
 5. Dauko tafasashshe macaroni ki sa a ciki ki juya sai ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya dauko shanye wa sai ki kawo alaiyaho (Karki yanka a dogo dogo za ki sa ) ki sa a ciki ki juya ki rufe su turaru sai ki sauke. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

Average: 3.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Matakai 5 na yin Chinese macaroni”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading