Skip to content

Yadda ake faten wake da dankali

Yadda ake faten wake da dankali
4
(2)

Faten wake abinci ne na gargajiya na al’ummar Hausaw da ake yi da wake, wanda aka fi sani da ”beans porridge” a turance. Abinci ne mai gina jiki sosai wanda ake ci a matsayin babban abincin rana ko na dare. Ana iya cin faten wake shi kadai, ko kuma a ci shi da biredi, fried plantain wato ”dodo” ko koko wato ”pap”.

Mu koyi yadda ake faten wake da dankali cikin matakai biyar masu sauki.

Abubuwan hadawa

  1. Wake (dafaffe)
  2. Dankalin turawa (dafaffafe)
  3. Jajjagen Tarugu da albasa (grated)
  4. Ganyen albasa (lawashi)
  5. Manja(mai kyau)
  6. Albasa
  7. Maggi(9ja pot)
  8. Kayan kamshi da dandano(Spices)
  9. Crayfish (in ana bukata)
  10. Gishiri

Yadda ake hadawa

  1. A wanke wake sannan a dafa shi har sai yayi laushi sosai. Zaki iya amfani da pressure pot don ya dafa shi cikin sauri kuma yayi laushi sosai.
  2. Ki sa tukunyanki akan wuta ki sa manja, sai ki kawo albasarki ki yanka a ciki ki soya sama sama.
  3. Sai ki dauko jajjagen tarugu da albasa ki sa a ciki ki juya.
  4. Sai ki kawo spices naki ki sa a ciki da su maggi da crayfish ki sa sai ki juya, anan sai ki kawo ruwan zafi kadan (idan a kwai ragowar ruwan dahuwar wakenki) ki sa ki rufe tukunya ki har sai Kinji Ya fara tafasa.
  5. Daga nan sai ki dauko wakenki tare da dankali ki sa a ciki ki juya a hankali ki rufe tukunyanki nadan wani lokaci.
  6. Daga karshe sai ki kawo ganyen albasarki ki sa a ciki, ki rufe tukunyanki na dan wani lokaci, sai ki sauke. A ci dadi lafiya

Sai mun hadu a girki na gaba.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×