Skip to content

Suyan dankali mai nama da kwai na musamman

Share |
Suyan dankali mai nama da kwai na musamman
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake suyan dankali mai nama da kwai. Wannan hadin dankali mai nama da kwai yana da dadi da kuma sauki wajen hadawa.

Abubuwan hadawa

  1. Dankalin (irish)
  2. Nama mai kyau 1/3 kilo
  3. Kwai 4
  4. Gishiri
  5. Man gyada
  6. Tsinken tsokale Hakori (toothpick)

Yadda ake hadawa

  1. Da farko ki fere dankalinki ki yanka a kwance sai ki wanke ki zuba a tukunya ki dora a wuta ki sa gishiri.
  2. Idan ya yi sai ki sauke, ki dauko namanki ki wanke ki tafasa da maggi, idan ya yi sai ki soya sama sama ki ajiye gefe.
  3. Sai ki dauko tsinken tsokale hakorinki, ki sa dankali daya da nama daya, a haka za ki yi ta jera su har sai kin kare.
  4. Sai ki fasa kwai a roba ki kada sosai ki sa manki a wuta, sannan ki dauko wannan dankalin ki na sawa a kwai, ki soya, idan ya yi sai a yi abin karyawa.

A ci dadi lafiya. Na gode.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading