Ga yadda ake dankali mai kabeji, mu koya ‘yanuwa. Wannan hadin dankali da kabeji yana da dadi da kuma armashi kuma abinci ne na fitan kunya.
Abubuwan hadawaa
- Dankalin turawa
- Kabeji (ki yanka a wanke da gishiri kadan a tsaneshi)
- Karas (ki gyara ki yanka shi)
- Koren tattasai (a wanke, a yanka)
- Tattasai (ki wanke, ki yanka)
- Tarugu (jajjagagge)
- Albasa(a yanka)
- Maggi
- Kayan kamshi
- Man gyada (yanda zai isheki suya)
- Gishiri
- Butter
Yadda ake hadawa
- Ki fere dankalin turawa ki yankashi irin yankan suya sai ki soya da man gyada tare da gishiri, sai ki tsane man dake jiki a matsani. Ajiye a gefe
- Ki daura tukunya akan wuta ki sa butter, idan ya narke ki sa albas a a ciki ki soya sama sam a sai ki kawo tarugu ki sa ki soya sama sama shima, ki kawo kayan kamshi da maggi (iya dandanon da zai miki) ki sa ki juya, bayan nan sai ki sa ruwa kadan (kamar cokali biyu zuwa uku).
- Sai ki dauko kabejinki ki sa a ciki ki juya ki rufe nadan wani lokaci, sai ki kawo koren tattasai da karas ki sa a ciki ki juya ki rufe na dan wani lokaci (amma ki rage wuta).
- Daga karshe sai ki dauko soyayyen dankalin da kika soyannan ki tuba a ciki ki juya a hankali sai ki sake rufe shi nadan wani lokaci kamar minti daya sai ki sauce. A ci dadi lafiya.
Karin bayani
za ki iya soya kwai ki sa a gefen dankalin mai hadi kamar yadda ki ka gani a hotonnan.