Skip to content

Yadda ake coconut puff puff

Share |
Yadda ake coconut puff puff
Add to Lists (0)
Please login to bookmarkClose

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake coconut puff puff. Wannan puff puff ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!

Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi 1½
  2. Kwakwa cokali biyu babba
  3. Yeast cokali 1 babba
  4. Madarar gari cokali biyu babba
  5. Gishiri kadan
  6. Suga cokali biyu babba
  7. Ruwan dumi kofi daya

Yadda ake hadawa

  1. Ki gyara kwakwan ki cire dattin bayan sai ki gurza ta a jikin abun goge kubewa ki ajiye a gefe. Sannan ki dauko flour ki tankade a babban kwano madaidaici, sai ki dauko kwakwa ki sa a ciki flour, suga, madara, gishiri kadan, sai yeast ki sa (amma ki tabbatar yeast din mai kyau ne).
  2. Sai ki zuba ruwan dumi kofi daya a ciki sai ki kwaba kamar na minti 5 (ki tabbatar kwabinki ya kwabu sosai) sai ki rufe ki kai rana ya tashi kamar minti 20. Za kuma ki iya sawa a oven ba tare da kin kunna ba (zai tashi a hakanma).
  3. Bayan ya tashi ki dauko ki sake buga shi sosai kamar minti 2 sai ki daura man gyada akan wuta idan ya yi zafi sai ki na diba ki na sawa ki na soyawa (amma ni nayi diban nawa kanana ne). Sai ki cire daga mai ki tsane shi.
  4. Daga karshe sai ki barbada sugar a kai (amma ba dole ba ne), shi kenan sai ci. A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
×