Skip to content

Yadda ake cabbage sauce

Bookmark (0)

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake cabbage sauce. Wannan cabbage sauce ne mai dadi ga kuma saukin hadawa. Uwargida ba a bawa yaro mai kiwuya!

Abubuwan hadawa

 1. Kabeji (ki yanka ki wanke da gishiri)
 2. Tsokar kaza (ki bare shi sala sala)
 3. Karas (ki gurza shi)
 4. Koren tattasai da tarugu (ki yanka)
 5. Lawashi (ki yanka)
 6. Albasa (ki yanka)
 7. Maggi
 8. Kayan kamshi
 9. Butter
 10. Tarugu (jajjaga)

Yadda ake hadawa

 1. Daura tukunyarki akan wuta ki sa butter ki yanka albasarki ki soya sama sama, sai ki kawo tsokar kaza ki sa a ciki ki juya ki soya sama sama.
 2. Sai ki dauko jajjagen tarugunki da albasa ki zuba a ciki shima ki soya sama sama Ki kawo maggi, kayan kamshi ki sa a ciki shima (iya dandano da zai miki), sai ki dan sa ruwan dumi kadan ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya ragu.
 3. Ki dauko kabejin ki ki sa ki juya ki rufe tukunya ki na dan wani lokacin kadan.
 4. Daga karshe, sai ki kawo karas, koren tattasai da lawashi ki sa a ciki ki juya ki rufe tukunyar ki na dan wani lokacin kadan, kamar minti 2, sai ki sauke.

How many stars is worth this recipe?

As you found this recipe interesting...

Follow us on social media to see more!

Share this recipe on social media.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free recipes remaining!
×