Skip to content

Lemon kankana da cucumber

Share |
Lemon kankana da cucumber
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ga yadda ake lemon kankana da cucumber cikin sauki. Wannan lemon na da saurin hadawa ga kuma dadi. Ba a bawa yaro mai kiwuya.

Abubuwan hadawa

  1. Kankana
  2. Cucumber kadan (dan ya kara mashi kamshi ne)
  3. Foster clerk (irin flavour da ki ke so)
  4. Kankara
  5. Ruwan sanyi

Yadda ake hadawa

  1. Ki fere kankana ki gyara shi ki cire bakaken kwallayen da ke ciki sai kin yanyanka kanana, ajiye gefe.
  2. Dauko cucumber ki fere bawon bayan ki cire abun tsakiyan (‘ya’yan cikin) ki yanka su kanana shima ajiye a gefe.
  3. Dauko blender ki zuba kankananki da cucumber shima ki sa a ciki sai ki kawo ruwan sanyi ki sa ki zuba foster clerk daidai zakin da zai mi ki, sai ki sa ruwan sanyi (ruwan da za ki sa ya danganta da irin kaurin da ki ke so, idan ki na so ya miki ruwa sai ki kara ruwa yanda zai isheki). Bayan kin kammala zuba komai sai ki markada har sai kinga ya yi laushi ya markadu sai ki zuba a kofi. Ki sa a fridge ya kara sanyi.

Karin bayani

Idan ki na so za ki iya tacewa ki sha iya ruwan lemon kankana ko kuma ki barshi haka ki sha. A sha dadi lafiya.

Rate the recipe.

Average: 3 / 5. Rating: 9

As you found it interesting...

Follow us to see more!

2 thoughts on “Lemon kankana da cucumber”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading