Skip to content

Yadda ake yam balls

Yadda ake yamballs
5
(4)

Ga yadda ake yam balls mu koya ‘yanuwa. Wannan recipe ne mai sauki da kuma dadi cikin ‘yan lokaci kadan uwargida za ki hada komai da komai.

Abubuwan hadawa

  1. Doya (dafaffafiyar doya)
  2. Nama (ki dafa sannan a daka shi )
  3. Flour
  4. Gishiri
  5. Kwai
  6. Tarugu
  7. Albasa (a jajjaga)
  8. Maggi (iya dandano da zai miki)
  9. Curry
  10. Kayan kamshi
  11. Man gyada (Na suya)

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko dafaffafiyar doyar ki kisa a turmi ki daka ta (sama sama dakan za ki yi) sai ki kwashe a kwano mai dan girma.
  2. Ki dauko dakakken naman ki kisa a cikin doyarki.
  3. Sai ki dauko jajjagen tarugunki da albasa ki zuba ciki
  4. Ki dauko kayan kamshi, gishiri kadan, curry, maggi ki sa a ciki.
  5. Sai ki juya sosai har sai ya hade jikinsa. 
  6. Sai ki dauko kwanki ki fasa ki yanka albasa da tarugu a ciki (bana sa gishiri domin kwan ya kama jikin doyan sosai) ki ajiye a gefe.
  7. Ki tankade filawarki ki sa a tire ko roba ki ajiye shima a gefe.
  8. Sai kina diban hadin doyar ki ki na mulmula shi (ya mulmulu sosai), sai ki bade shi da filawa. Haka za kiyi da sauran hadin doyarki har ki gama.
  9. Sai ki daura man gyada akan wuta idan ya yi zafi sai kina daukan mulmulalliyar doyarki (wanda ki ka bade da filawa) ki na sawa a cikin kwanki (wanda ki ka buga ki ka yanka masa albasa da tarugu ciki) ki na sawa a mai ki na soyawa har ya soyu (golden brown). Haka za ki yi da sauran har ki gama da doyarki. Aci dadi lafiya.

How many stars is worth this recipe?

We are sorry that this recipe was not as good as you wanted it to be!

Please, provide us with your feedback to improve it.

Write your feedback in the box below and then submit.

You cannot copy content of this page
×