Skip to content

Yadda ake tumki sauce

Share |
Yadda ake tumki sauce
Add to Lists (0)
Please login to bookmark Close

Ku koyi yadda ake tumki sauce cikin sauki. Domin hada wannan sauce ana bukatan kayan hadi takwas, hadawa ma cikin matakai takwas.

Abubuwan hadawa

  1. Kifi banda
  2. Dafaffafen kayan ciki (iya tumbi za ki amfani dashi )
  3. Maggi
  4. Gishiri kadan
  5. Kayan ?amshi
  6. Tarugu
  7. Albasa
  8. Man gyada ko butter

Yadda ake hadawa

  1. Ki dauko kifi banda ki bare tsokan ki cire kayan jiki. Sai ki daura tsokar akan wuta ya tafasa ko ki jika da ruwan zafi ki ajiye nadan wani lokaci har sai ya yi laushi sosai. Ajiye a gefe.
  2. Ki dauko kayan ciki (tumbi) dama kuma kin dafa shi ya dahu ya yi laushi, sai ki dauko ki yanka shi kanana kanana ki ajiye a gefe.
  3. Dauko tarugu ki jajjaga, ki yanka albasa sosai a wani kwano daban. Ajiye a gefe
  4. Albasa mai lawashi itama ki yanka tare da koren tattasai ajiye a gefe shima daban.
  5. Sai ki daura tukunya ko non stick pan naki akan wuta ki sa butter ko man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama. Ki dauko tarugu ki sa ki soya sama sama shima.
  6. Sai ki dauko kayan ciki (tumbi) da kifi banda, kayan kamshi, maggi( iya dandano da zai miki ) gishiri kadan ki sa sai ki juya.
  7. Ki kawo albasa (wanda ki ka yanka daban) ki sa sannan ki juya nadan wani lokaci sai ki kara ruwa (ruwan za ki iya amfani da ruwan da kika jika kifin dashi) kadan (dai dai yanda ba zai ruwa ba kuma ba zai yi kamar ba don ana san shi da dab romo romo )
  8. Sai ki rufe tukunya ki na dan wani lokaci. Daga karshe ki dauko lawashi ki tare da koren tattasai ki sa juya nadan wani lokaci Saiki sauke.

Rate the recipe.

As you found it interesting...

Follow us to see more!

1 thought on “Yadda ake tumki sauce”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
2
Free daily recipes remaining!
×
×