Skip to content

Yadda ake spicy peppered chicken

Share |
spicy peppered chicken
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Barkanmu da saduwa a Bakandamiya kitchen. A girkinmu na yau za mu koyar da yadda ake peppered chicken. Ga shi kamar haka dalla-dalla:

Abubuwan hadawa

 1. Kaza (agric chicken)
 2. Albasa
 3. Lawashi
 4. Seasoning
 5. Spices
 6. Gishiri
 7. Tandoori kitchen spice
 8. Citta (ginger)
 9. Tafarnuwa (garlic)
 10. Maggi
 11. Tattasai
 12. Tarugu
 13. Mai

Yadda ake hadawa

 1. Da farko dai ya kasance kin wanke kazanki tas kin cire mata duk wani datti, Ki zuba kazan a tukunya ba tare da kinsa mata ruwa ba (ki sani cewa kajin turawa ba su son ruwa sosai).
 2. Ki wanke albasa mai yawa tare da lawashinta ki zuba a kai dan ki tafasa kazar, ki sa seasonings da spices na ki, ki sa gishiri da tandoori Kitchen spice da Kuma citta da tafarnuwa duk don ki cire karnin kazar ki, ki rufe ki bata minti 8 ko 10 don ta tafasa.
 3. Ki juya don maggi ya ji ko ina, Ki zube a wani bowl asa man gyada ya yi zafi sosai sai a soya wannan kazar har sai kinga ta yi ja sosai dan ta yi dadi, za kuma tafi dadewa a ajiye, ba kamar in kin soya ta ne sama sama ba.
 4. Bayan kin gama soyawa, sai ki rage mai kadan ki zuba chopped tattasai da tarugu, ki sa albasa da lawashi, sai seasoning na ki, ki tabbatar ya ji albasa sosai, sai ki soya sama sama kamar mintina 8 zuwa 10 sai a sauke.
 5. A karshe, sai ki juye sauce din a cikin soyayyar kazan ki. Shike nan kin gama.
  Mai karatu wannan shine yadda ake spicy peppered chicken. Sai mun hadu a girki na gaba. Amma kafin nan, za a iya duba:Yadda ake fried rice mai kaza da yadda ake shinkafa da vegetable sauce da sauransu.

Rate the recipe.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading