Skip to content

Yadda ake hadin shinkafa da vegetable sauce

Share |
Yadda ake hadin shinkafa da vegetable sauce

Mu koyi yadda ake hadin shinkafa da vegetable sauce cikin sauki. Wannan hadin shinkafar da sauce akwai dadin gaske ga shi kuma kalar fitar kunya ce!

Abubuwan hadawa

  1. Kayan lambu (karas da peas da mushroom na kanti)
  2. Albasa
  3. Tattasai
  4. Kayan kamsh
  5. Maggi
  6. Shinkafa
  7. Green pepper
  8. Kwai
  9. Hanta

Yadda ake hadawa

Shinkafar

Ita wannan shinkafar za ki dafa farar shinkafa daban, sai ki soya dan albasa da green pepper da kwai, sai ki sa maggi chicken sannan ki sa shinkafar ki juya abari ya turara sai a kwashe!

Vegetable sauce

Da farko za ki soya albasa, ki kawo kayan lambu ki saka ki dan sa ruwa, ki kawo kayan kamshi da jajjagen tattasai ki saka inda tarugu ki saka, ki sa maggi star, sai ki kawo hantanki ki saka!

Ki rufe ki bar shi a low heat (wuta kasa-kasa) na minti biyar!
A ci dadi lafiya!  

Add to Lists (0)
ClosePlease loginn

No account yet? Register

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page