Skip to content

Yadda ake special vegetable soup

Share |
special vegetable soup
Add to Lists (0)
ClosePlease login

No account yet? Register

Ku koyi yadda ake special vegetable soup mai armashi. Wannan vegetable soup recipe ne mai saukin bi da kuma dadin gaske.

Abubuwan hadawa

 1. Yakuwa (ki yanka)
 2. Alaiyaho (ki yanka)
 3. Water leave (ki yanka)
 4. Tarugu (ki yanka)
 5. Albasa (ki yanka)
 6. Tumatur (ki yanka)
 7. Kifi dafaffe
 8. Karas
 9. Kayan kamshi
 10. Maggi
 11. Man gyada
 12. Ruwan silalen kifi kadan

Yadda ake hadawa

 1. Ki dauko ganyenki da ki ka yanka su ki wanke da gishiri ki tsanesu a matsami ajiye a gefe.
 2. Ki daura tukunya akan wuta ki sa man gyada ki yanka albasa ki soya sama sama.
 3. Sai ki kawo tarugu ki sa ki kawo albasa sosai (wanda ki ka yanka a baya) ki sa ki juya ki soya sama sama shima, sannan ki kawo ruwan silalen kifinki ki sa a ciki ki juya.
 4. Sai ki kawo kayan kamshi da gishiri, maggi iya dandano da zai mi ki da dafaffafen kifi ki sa, ki juya, rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya ragu sai ki kawo ganyenki (wanda ki ka wanke a baya) ki sa ki juya, ki rufeshi nadan wani lokaci.
 5. Daga karshe sai ki kawo karas da yankakken tumatur ki sa a ciki, ki juya yadan turara a ciki sai ki sauke. A na iya cin wannan miya tare da tuwon shinkafa, ko couscous, ko farar shinkafa da dai sauransu .A ci dadi lafiya.

Rate the recipe.

Average: 2.7 / 5. Rating: 11

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page
3
Free daily recipes remaining!
×

Discover more from Bakandamiya Kitchen

Subscribe now to keep reading and get access to the full archive.

Continue reading